in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Afirka ta kudu ya gana da Yang Jiechi
2015-10-11 13:50:50 cri
A jiya 10 ga wata bisa agogon wuri, shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma ya gana da Mr. Yang Jiechi, wakili mai kula da harkokin diflomsiyya a majalisar gudunarwa ta kasar Sin a birnin Johnnesburg, babban birnin kasar.

A yayin ganawar, da farko, Mr. Zuma ya nemi Mr. Yang Jiechi da ya mika gaisuwa da fatansa na alheri ga shugaba Xi Jinping na kasar Sin. Sannan ya bayyana cewa, kasar Sin ta kasance wani muhimmin ginshiki ga kokarin tabbatar da kuma shimfida zaman lafiya da neman bunkasuwa a duk duniya baki daya, kuma abokiyar arziki ce ta yin hadin gwiwa da dukkan kasashe masu tasowa za su iya yin dogara da ita. A yayin jerin tarurukan koli da aka shirya a MDD kwanan baya, shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarwari iri iri, inda ya zana wata kyakkyawar hanya kan yadda za a yi hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa da kuma bunkasa irin wannan hadin gwiwa da neman ci gaban duk duniya baki daya. Bisa wannan halin da ake ciki, taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da za a shirya a watan Disamba yana da ma'ana mai muhimmanci. Ya kamata kasashen Afirka su kara yin kokarin bunkasa dangantaka a tsakaninsu da kasar Sin, kuma su kara yin hadin gwiwa da kasar Sin ta yadda za su iya kara bunkasa tattalin arziki da zamantakewa da sauran muhimman fannonin nasu.

Bugu da kari, Mr. Zuma ya ce, yana jiran ziyarar Xi Jinping a kasar Afirka ta kudu da hannu bibbiyu domin shugabantar wannan taron koli tare. Yana fatan sassan biyu za su iya shirya kome da kome game da wannan taron koli, ta yadda za a iya cimma nasarar wannan taron kamar yadda ake fata. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China