Kungiyar dai na maida hankali koda yaushe wajen yin sintiri da fadakar da al'ummomin dake kusa da yankunan namun daji, a cewar ministan kula da harkokin muhalli na Afrika ta Kudu, Edna Molewa.
Dabarun kirkirowa na al'ummomi nada muhimmanci wajen yaki da kasuwancin namun daji na bayan fage, kuma kungiyar Bakaken Mambas ta jaddada karfinta na kwarewa da niyyarta a gida, in ji sakatare janar na MDD da kuma babban darektan tsarin PNUE, Achim Steiner.
Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon zai bada kyautar da hannunsa ga wannan kungiyar a ranar 27 ga watan Satumba a birnin New York.
An kafa kungiyar Bakaken Mambas a shekarar 2013, tana kunshe mata 25 da namiji daya da suka fito daga al'ummomin yankunan dake kusa da kebabbun wurare na namun dajin kasa dake arewa maso gabashin Afrika ta Kudu.
Tun lokacin da aka tura su a sansanin kiyaye namun daji na Balule Nature Reserve, a arewacin gundumar Limpopo, bauna hudu ne kawai mafarauta suka kashe. Kungiyar ta taimaka wajen cafke mafarauta shida, da fidda tarko fiye da dubu daya tare da lalata dakuna biyu da ake amfani da su wajen dafa naman namun daji.
Bakaken Mambas na kasancewa wani muhimmin misali na alkawarin gwamnatin Afrika ta Kudu, bangaren masu zaman kansu da al'ummomin wuraren wajen kawar da farautar bauna ta bayan fage, in ji mista Molewa. (Maman Ada)