in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin baje kolin litattafai na kasar Sin ya zama wata gada ta yin musayar al'adu tsakanin Sin da Birtaniya
2015-10-20 20:55:49 cri

A yau ne aka bude bikin baje kolin littattafan kasar Sin na shekarar 2015 a shagon sayar da litattafai na Hatchards dake birnin London, wanda ke da tarihi fiye da daruruwan shekaru, bikin ya kuma samarwa masu karatu 'yan Birtaniya wasu fitattun litattafai na kasar Sin.

A saran kwashe kwanaki 10 wato daga ran 19 zuwa 28 ana gudanar da wannan biki. Yayin bikin, masu karatu 'yan Birtaniya za su samu wasu shahararrun littattafai da Sin ta buga cikin 'yan shekarun baya wadanda suka yi suna a duniya.

A yayin bude bikin, mataimakin direktan ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin Mista Guo Weimin ya ce, yana fatan tare da imani cewa, wannan biki zai samarwa masu sha'awar karance-karance na kasar Bitaniya fitattun litattafan kasar Sin, wadanda za su taimaka musu kara fahimtar kasar Sin tare da kaunar kasar Sin, matakin da zai sanya 'yan kasar karfafa zumunci da kara yin mu'ammala da hadin gwiwa tsakaninsu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China