A yayin da babban jami'in kwamitin cinikayya tsakanin kasashen Birtaniya da Sin Stephen Phillips ke zantawa da wakilinmu, ya ce, ziyarar shugaban kasar Sin a Birtaniyan za ta karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen biyu, kuma 'yan kasuwa da masu masana'antu za su ci gajiyar wannan dangantaka.
Stephen Phillips ya ce, a cikin 'yan shekarun nan, kamfanonin kasar Sin da dama sun zuba jari a Birtaniya, kuma Birtaniyar ta alkawarin bude kofa don yin maraba da masana'antun Sin da su zuba jari a kasar. Masana'antun Sin da dama ba ma kawai sun cimma nasara wajen zuba jari a Birtaniya ba, har ma sun shiga kasuwanni a kasashen Turai ta Birtaniya, ta yadda aka gaggauta aikin raya masana'antun Sin a kasashen waje.(Bako)