in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masarautar Burtaniya ta shirya gagarumar tarba ga shugaban kasar Sin da ke ziyara a kasar
2015-10-20 20:44:47 cri

Da tsakar ranar yau ne aka fara wani gagarumin bikin gargajiya na maraba da sarauniya Elizabeth ta biyu ta shirya wa shugaban kasar Sin Jinping na kasar Sin da a hanlin yanzu ya ke ziyara a kasar Burtaniya, inda manyan iyalan gidan saraudar Burtaniya da shugabannin siyasa suka kalli jerin gwanon dawakin da suka ratsa tsakiyar birnin London.

Yarima Charles a madadin sarauniya da iyalan masarautar da yarima na wales da gimbiyar Cornwall ya jagoranci faretin dawakin da aka shirya wa shugaba Xi na kasar Sin da mai dakinsa Peng Liyuan.

Tun da sanyi safiya ne dubban jama'a suka yi layi a gaban fadar Buckingham da titunan da ke kewaye da fadar, don yiwa babban bakon maraba. Shugaba Xi shi ne shugaban kasar Sin na farko da ya kawo ziyara Burtaniya a cikin shekaru 10 da suka gabata, matakin da zai bunkasa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Xi wanda ya samu rakiyar Duke na Edinburgh ya duba faretin ban girnan da aka shirya masa, kana daga bisani shi da sarauniya da Basaraken suka shiga jerin gwanon da ya tashi daga Mall zuwa fadar Buckingham, suna tafe ana rera taken kasar Sin.

An kuma harba bindiga sau 41 don nuna gaisuwa ga babban bakon.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China