Sin da Afirka ta Kudu sun cimma matsayi kan yadda za a gudanar da taron kolin Johannesburg
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a yayin taron maneman labarai da aka yi a yau Litinin cewa, kwanan baya, wakilin majalisar gudanarwar kasa ta Sin Yang Jiechi ya kai ziyarar aiki kasar Afirka ta Kudu a hukunce, inda ya tattauna da wakilan kasar Afirka ta Kudu kan yadda za a gudanar da taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da za a yi a watan Disamba na bana, da kuma harkokin dake shafar ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai kasar Afirka ta Kudu da dai sauransu, ta yadda za a samu nasarar gudanar da taro da kuma ziyarar aiki da Xi Jinping zai kai a kasar.
Kasar Afirka ta Kudu na mai da hankali sosai kan ziyarar aiki da Yang Jiechi ya kai a kasar, inda bangarorin biyu suka cimma matsayi daya kan harkoki da dama, suna kuma ganin cewa, taron kolin da za a yi a birnin Johannesburg na da muhimmanci matuka wajen zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, da kuma raya dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. (Maryam)