Yayin ganawar, Mista Yang ya ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyarar aiki a Amurka a wata mai zuwa, wadda ke da babbar ma'ana ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da halin da duniya ke ciki. A cewarsa, ya kamata kasashen biyu sun kara hadin gwiwa a fannoni daban-daban saboda ganin sarkakiyar halin da dunya ke ciki.
A nata bangare, Madam Rice ta ce shugaban kasar Amurka Barack Obama ya nuna kyakkyawar fata ga ziyarar da shugaba Xi zai yi, sannan kuma yana jiran musanyar ra'ayi da shugaba Xi Jinping kan wasu manyan abubuwan duniya dake jawo hankalinsu. (Amina)