A jawabinsa Yang Jiechi ya bayyana cewa, tuni dai shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki a kasar Amurka. Shugabannin kasashen biyu sun tabbatar da makomar raya huldar dake tsakanin kasashen nasu, inda suka inganta hadin gwiwarsu a harkokin shiyya-shiyya da kuma duniya baki daya. A nan gaba ne, ake sa ran bangarorin biyu za su yi kokarin aiwatar da abubuwan da shugabannin biyu suka cimma ra'ayi daya a kansu domin inganta huldar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata.
Bugu da kari, Anthony Blinken ya ce, nasarar ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai a kasar Amurka ta bayyana wa duniya cewa, kasashen Amurka da Sin suna iya hada kai a kan wasu manyan fannoni. Kasar Amurka tana son tabbatar da sakamakon da aka samu a yayin wannan ziyara, domin ciyar da huldar dake tsakanin kasashen 2 gaba.(Lami)