Yang Jiechi ya bayyana cewa, a shekarar 2013, cikin ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a wasu kasashen Afirka a karo na farko, ya fidda manufofin gudanar da ayyukan dake shafar harkokin kasashen Afirka bisa nuna gaskiya, adalci da kuma zumunci yadda ya kamata. Kuma babban take shi ne, a hada aikin taimaka wa kasashen Afirka wajen cimma burin samun zaman lafiya, tattalin arziki da dauwamammen ci gaba da aikin neman bunkasuwar kasar Sin tare, ta yadda za a iya cimma moriyar juna da kuma neman ci gaba cikin hadin gwiwa.
Kaza lika, za a gudanar da taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka a nahiyar Afirka a karo na farko, lamarin dake da muhimmiyar ma'ana wajen ciyar da dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka gaba daga dukkan fannoni, da kuma inganta dauwamammen ci gaban duniya cikin yanayin daidaituwa. Kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasar Afrika ta Kudu da sauran mambobin kasashen Afirka guda 50 wajen gudanar da harkokin taron kolin din cikin yanayi mai kyau, bisa akidar nuna adalci da yin hadin gwiwa, ta yadda za a iya karfafa hadin gwiwar kasashen Sin da Afirka da kuma ciyar da hadin gwiwar Sin da Afirka gaba. (Maryam)