in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yang Jiechi ya gana da ministar harkokin wajen Afrika ta kudu
2015-10-10 08:56:38 cri

A jiya Jumma'a ne memba a majalisar gudanarwa ta kasar Sin Yang Jiechi ya gana da ministar harkokin wajen Afrika ta kudu Maite Nkoana-Mashabane.

Yayin tattaunawar tasu, Yang Jiechi ya bayyana cewa, a shekarun baya huldar dake tsakanin kasashen Sin da Afrika ta kudu ta samu bunkasuwa sosai, ya kara da cewar, kasar Sin tana son yin hulda da Afrika ta kudu wajen tabbatar da abubuwan da shugaban kasar Sin Xi Jinping da kuma takwaransa na kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma suka cimma matsaya a kai, domin ci gaba da inganta huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu.

Bugu da kari, Yang Jiechi ya ce, wannan shekara na da muhimmanci sosai a cikin tarihin bunkasuwar huldar Sin da Afrika ta kudu. Shugaba Xi Jinping zai halarci taron koli na dandalin tattaunawa na hadin gwiwar Sin da kasashen Afrika da za a yi a kasar Afrika ta kudu, kuma zai kai ziyarar aiki a kasar a nan gaba. Kasar Sin ta jinjinawa aikin share fage da kasar Afrika ta kudu ta yi, tana fatan bangarorin biyu za su rika tuntubar juna domin tabbatar da ganin an gudanar da wannan taro lami lafiya.

A nata bangaren Maite Nkoana-Mashabane, ta bayyana cewar Afrika ta kudu ta gamsu bisa kyakkyawar hulda dake tsakaninta da kasar Sin. Kasar Afrika ta kudu ta dora muhimmanci sosai kan jerin jawabai da kuma shawarwarin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayar a yayin taron MDD a kwanan baya, kuma tana fatan Mr. Xi zai shugabanci taron koli tare da Jacob Zuma, sannan tana son yin musayar ra'ayoyi da kasar Sin da nufin inganta hulda dake tsakanin kasashen biyu.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China