Ghirmay Ghebreslassie ya kammala wasan Marathon din cikin awoyi 2 da mintoci 12 da dakika 28, sai kuma Yemane Tsegay wanda ya kai matsayi na takwas cikin gasar fid da gwani ta duniya ta wasan guje-guje da tsalle-tsalle da aka yi a shekarar 2013 ya samu lambar yabo ta azurfa cikin gasar na wannan karo, yayin da dan wasan kasar Uganda Munyo Solomon Mutai ya samu lambar yabo ta tagulla.
Haka kuma, cikin gasar na wannan karo, kasar Kenya wadda ta kasance gaba a fannin wasan guje-guje da tsalle-tsalle a kasashen duniya, ta aike da 'yan wasa guda uku domin halartar gasar a ciki hadda Dennis Kimetto wanda yake da matsayin bajintar duniya a hannunsa, amma Dennis Kimetto da wani dan wasan kasarsa ba su iya kammala gasar ba, dayan dan wasan kasar Kenya Paul Korir ya zama a matsayi na 22 cikin gasar da aka yi a yau. (Maryam)