Gasar kokowar gargajiya karo na 35 ko kuma takobin kasa, gasar motsa jiki mafi samun karbuwa a kasar Nijar za ta gudana daga ranar 7 zuwa 16 ga watan Maris mai zuwa a jihar Diffa dake kuryar gabashin kasar, a wani labarin da ya fito daga wata majiya mai tushe a ranar Lahadi a birnin Yamai.
A cewar ministan wasannin motsa jikin kasar Nijar, gasar ta wannan karo za ta kasance bisa taken sasanta bangarori daban daban bisa sabon kundin dake tafiyar da dokokin wannan wasa mafi karbuwa a kasar Nijar.
Ministan ya jaddada cewa, gasar kokowar gargajiya ta kasa, bayan kasancewa hanyar motsa jiki, haka kuma ta zama wani tushen karfafa hadin kasa da jituwar al'ummar kasar Nijar baki daya.
Tun zamanin da, kokowar gargajiya ta zama wasan motsa jiki da al'adu da 'yan kasar Nijar suke yi bayan an kare girbin albarkatun noma.
A gasar farko da aka yi a shakarar 1975 a jihar Tahoua, wanda kuma Yacouba Kantou na jihar Maradi ya lashen takobin da filin wasan kokowa na jihar yake dauke da sunansa. Gasar kokowa ta baya, an shirya ta a birnin Yamai. (Maman Ada)