in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dan wasan Kenya ya kafa sabon tarihin gasar gudun dogon zangon duniya a Berlin
2014-09-29 14:45:43 cri

Dennis Kimetto, 'dan wasa daga kasar Kenya ya kafa wani sabon tarihi na gasar gudun dogon zango na duniya, yayin da ya kammala tseren nasa a cikin awowi 2 da minti 2 da dakika 57, a wata gasar tseren gudu da aka yi a Berlin dake kasar Jamus. Kimetto ya zamanto mutum na farko a duniya da kammala gudun nasa kasa da awowi 2 da minti 3.

Kimetto na daga cikin wasu maza 7, wadanda suka balle bayan wani gudun kilomita 20, daga nan sai ya shiga takarar gudun kilomita 4, tare da wani 'dan kasar Kenya Emmanuel Mutai, kuma a karshe ya lashe gasar gudun tare da kafa tarihin kammalawa a kan lokaci.

Kididddiga ta nuna cewar, yayin gasar gudun dogon zangon duniyar ta bara, wani 'dan kasar Kenyan ne Wilson Kipsang ya lashe wasan a inda ya kammala gudun a cikin awowi 2 da minti 3 da dakika 23.

Kimetto, 'dan shekaru 30, kamin ya shiga gasar gudun dogon zango ta duniya shi manomi ne a wani yanki mai fama da talauci. Ya fara sana'ar gudu a yayin da yake sama da shekarar 20 a duniya, kuma ya fara samun nasarar ne a yayin da ya ci gasar gudu ta Nairobi a shekarar 2011, kuma daga nan ne a shekarar 2012, ya yi na biyu a gasar gudun dogon zango ta duniya wadda aka yi a Berlin. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China