in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude babbar gasar wasannin motsa jiki ta kasar ta Sin karo na sha biyu a birnin Shenyang
2013-08-31 18:39:58 cri

Da yammacin Asabar 31 ga watan nan ne aka bude babbar gasar wasannin motsa jiki ta kasar ta Sin karo na sha biyu a birnin Shenyang, da ke lardin Liaoning.

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ne ya kaddamar da bude gasar, tare da bayyana fara gudanar gasar wasannin motsa jikin a hukunce.

A nasa jawabi na bikin bude gasar, shugaban kwamitin shirya gasar wasannin motsa jikin Liu Peng, ya bayyana cewa cikin shekaru 54 da suka gabata, wato lokacin da aka kafa gudanar da wannan gasa, an yi ta kyautata ta, kuma ta kawo ci gaba mai tarin yawa ga aikace-aikacen wasannin motsa jiki a fadin kasar ta Sin.

Tawagogin 'yan wasannin motsa jiki guda 38 da suka kunshi 'yan wasa 9,770, daga sassan kasar Sin daban daban ne dai suka halarci gasar ta bana. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China