Wasannin kasa da kasa na gasar kwallon rugby na Afrika rukuni na biyu na shiyyar yammacin Afrika, sun soma tun ranar Litinin da safe a filin wasannin motsa jiki na janar Seyni Kountche dake birnin Yamai.
Wannan gasa ta cigaban gamayyar Afrika ta wasannin rugby ta kunshi kasashe shida wato Benin, Burkina-Faso, Ghana, Mali, Togo da Nijar.
A gasar bude fage a ranar Litinin, kasar Nijar ta doke kasar Benin da ci 48 da 0, kasar Nijar dai ta shiga gaba a wasan rugby a wannan shiyya.
A cewar shugaban kungiyar wasan rugby ta kasa, Hamadou Nouhou, kungiyar 'yan wasan Nijar "Les Zebus" ta halarci gasar ta farko a shekarar 2005 da kungiyar wasan rugby ta Afrika mai taken "Top 16" a kasar Burkina Faso, sannan a shekarar 2006, kasar Nijar ta shirya gasar rugby kuma ta lashe a Yamai. Tun daga wannan lokaci, kasar Nijar ta cigaba da nuna kwarewarta a wasannin kasa da kasa tare da daukar kofi uku na gasar cikin kofin rugby na Afrika rukuni na biyu a shekarar 2006 a Nijar, 2008 a Ghana da 2009 a Togo.
Haka kuma kasar Nijar ta samu matsayi na biyu a gasannin rugby na shekarar 2010 da ta 2011 a Bamako, kafin ta zama zakaran Afrika na rugby na matsayin gaba a shekarar 2012 a kasar Togo.
Jerin lambobin yabo ya baiwa Nijar damar daukar matsayin gaba na rukunin farko. Haka kuma Nijar za ta halarci gasar cin kofin Afrika rukunin farko a birnin Yamoussoukro na kasar Cote d'Ivoire daga ranar 21 zuwa 28 ga watan Yuli mai zuwa. (Maman Ada)