in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi gasar harshen Sinanci karo na biyu a jami'ar Legas dake Najeriya
2013-03-16 19:46:40 cri

Ranar Jumma'a 15 ga wata ne, aka yi gasar harshen Sinanci mai taken "Chinese Bridge" karo na biyu a kwalejin Confucius na jami'ar Legas dake Najeriya.

Dalibai sama da dari uku daga makarantun firamare, sakandare, da kuma jami'o'i sun yi takara a fannoni guda uku, wato ilmin da ya shafi kasar Sin, rera wakokin kasar Sin, gami da yin raye-rayen kasar Sin. Karamin jakadan Sin dake Legas, Mista Liu Xianfa, shugabar kwalejin Confucius na jami'ar Legas malama Jiang Lirong, da kuma shehun malami daga sashin nazarin harsuna da harkokin Asiya da Afirka Oladipo Ajiboye sun halarci bukin.

A cikin gasar ilmin kasar Sin, daliban Najeriya sun yi kokarin amsa tambayoyin da suka shafi ilmin tarihi, al'adu, labarin kasa, siyasa, tattalin arziki, da kuma zaman rayuwar al'umma na kasar Sin. Sa'an nan a yayin gasannin rera wakokin kasar Sin da kuma yin raye-rayen kasar Sin, matasan sun sanya tufafin gargajiya masu kyan-gani, inda kwarewarsu a fannin rera wakokin Sinanci da yin raye-rayen gargajiya na kasar Sin ya baiwa masu kallo mamaki sosai.

A karshe dai, dalibai daga makarantar firamare ta Ladybird, da makarantar sakandare ta Grace, da kuma jami'ar Legas sun samu lambobin yabo.

Kamar yadda karamin jakadan Sin dake Legas Mista Liu Xianfa ya ce, yawancin mutanen da suka halarci gasar a wannan karo matasa manyan gobe ne. Yana fatan ta hanyar yin mu'amala da cudanya a fannin harshe, musamman ma tsakanin matasa, dangantakar abuta tsakanin Sin da Najeriya za ta ci gaba da inganta.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China