Hukumar wasan kwallon tebur ta duniya ta baiwa Najeriya mai masaukin bakin gasar cin kofin Afrika na wasan kwallon tebur a shekarar 2014 a karo na farko, tuni dai aka fara gudanar da gasar a babban filin wasa na Teslim Balogun dake birnin Lagos na Najeriya. Za'a gudanar da gasar ne tsakanin ranar 23 zuwa 26 ga watan Yuni.
Ana sa rai cewa, Omar Assar, 'dan kasar Masar wanda ya taba samun kyautar zakara a gasar kwallon tebur ta Afrika, shi ma zai shiga gasar ta Lagos.
Sauran kasashe da za su taka rawa a gasar sun hada da Singapore, Masar, Rasha, Benin, Congo Brazzaville, da kuma jamhuriyar damokradiyya ta Congo, Kamaru, Ghana, Libya, Luxembourg, Morocco, Saliyo, Togo, Tunisia da kuma Najeriya, wacce ita ce mai masaukin gasar wasan.
Hukumar kwallon tebur ta duniya ta jera sunayen alkalan wasa har 36, domin shiga tsakani a wasan, wanda za'a yi kwanaki 4 ana yi.
Hukumar ta zabi alkalan wasan daga Najeriya, Ghana, Algeriya, Libya, Togo, Congo Brazzaville, da kuma Benin domin sa ido a wasan. (Suwaiba)