in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta dauki nauyin gasar Airtel ta Afrika
2013-09-09 10:38:44 cri

Ministan wasanni na Najeriya Bolaji Abdullahi da ministan kula da al'amuran mata Hajia Zainab Maina za su jagoranci manyan jami'an gwamnati da na sauran kasashen waje domin halartar bikin bude gasar cin kofin kwallon kafa ta Airtel da za ta wakilci nahiyar Afrika baki daya a jihar Ikkon kasar tsakanin ranar 16 zuwa ta 22 ga watan nan da muke ciki.

Ita dai kungiyar kwallon kafan ta Airtel, wannan ne karo na biyu kuma mafi girma na 'yan kasa da shekaru 17 da aka lura, yana kula da jinsi ganin yana da sashen mata kamar yadda wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ya nuna masu shirya gasar sun tabbatar da cewa, kungiyoyi daga kasashen Afrika 16 suka nuna sha'awarsu na halartar gasar.

Babban jami'in kamfanin sadarwa na Airtel Segun Ogunsanya ya ce, kamfaninsa a shirye yake don dauki nauyin matasa daga nahiyar ta Afrika da sauran manyan baki da suke wakiltar kasashen nasu dake Najeriya.

Ita dai wannan gasar da kamfanin sadarwa na Airtel ya shirya tana da zummar ba da kwarin gwiwwa ne tare da taimakawa matasa sun inganta sha'warsu na buga kwallon kafa a rayuwarsu. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China