in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar tsaron Sin ta gudanar da bikin murnar cika shekaru 88 da kafuwar rundunar sojan kasar
2015-07-31 21:01:58 cri

Ma'aikatar tsaron kasar Sin ta gudanar da wata liyafa a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing a ranar Juma'ar nan, domin murnar cika shekaru 88 da kafuwar rundunar sojan kasar Sin.

Mamba a majalisar gudanarwa, kuma ministan tsaron kasar Sin Mr Chang Wanquan ya bayyana cewa wannan shekara da muke ciki ta cika shekaru 70 da samun nasarar yakin kin harin maharan Japan, ta kuma cika 70 da samun nasarar yaki da ra'ayin nuna karfin soja. A daidai wannan muhimmin lokaci ne kuwa ake cika shekaru 88, da kafuwar rundunar sojan kasar Sin.

Ya ce a cikin wadannan shekaru 88 da suka gabata, rundunar 'yantar da jama'ar kasar Sin ta yi iyakacin kokarin ta na raya kai, ta ba da gudunmawa wajen 'yantar da jama'ar kasar Sin, tare da samun wadata a kasar baki daya. Runduar ta kuma nace ga ra'ayin wanzar da zaman lafiya, da samun bunkasuwa, da hadin gwiwa, da samar da moriya ga juna, inda ta shiga wasu ayyuka na kasa da kasa, ciki hadda ayyukan kiyaye zirga-zirgar jiragen ruwa na kasa da kasa, da hadin gwiwa da sauran kasashe wajen yaki da ta'addanci, da rigakafin bala'u da cututuka da sauransu. A daya bangaren kuma ta taka rawar gani yadda ya kamata, a fannin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyya-shiyya da ma duniya baki daya.

Mr Chang ya kara da cewa, samun zaman lafiya a maimakon yaki, samun hadin gwiwa a maimakon yin gaba da juna buri ne na daukacin jama'ar duniya. Ko da yake rundunar sojan kasar Sin ba ta tsoron yake-yake, duk da haka tana da matukar kaunar zaman lafiya. Don haka za ta nacewa manufar tsaron kasa ta kare kai, tare da zurfafa hadin gwiwa da mu'ammala da sojojin kasa da kasa. Za kuma ta dauki karin nauyi gwargwadon karfinta, ta kuma ba da gudunmawa wajen kiyaye zaman lafiyar duniya, da samun bunkasuwa a duniya baki daya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China