Geng Yansheng ya ce, daga 16 zuwa 19 ga watan nan ne mataimakin shugaban hukumar kula da soja na kasar Sin Fan Changlong ya ziyarci kasar Austraila, inda ya gana da shugabannin gwamnati, hukumomin kiyaye tsaro da rundunonin sojojin kasar, tare da cimma matsayi daya kan bunkasa dangatakar soja tsakanin kasar Sin da Australia, sannan ya ziyarci sansanin sojin ruwa, hedkwatar sojan kasa da kuma hedkwatar ayarin jiragen ruwa ta kasar Australia.
Bugu da kari, a yayin ziyararsa a kasar, kasashen biyu sun sanar da gudanar da atisayen sojojin kasa tsakanin kasashen Sin, Australia da Amurka a kasar Australia a watan Oktoba mai zuwa a hukunce. Sa'an nan kuma, kasashen uku za su yi shawarwari don shirya ayyukan dake shafar wannan atisayen soja.
Wannan shi ne karo na farko da za a gudanar da atisayen soja tsakanin wadannan kasashen uku. (Maryam)