Wannan dai shi ne karo na 9 da kasar Sin ta gabatar da takardar bayani kan aikin tsaron kasa, tun bayan shekarar 1998, kuma ita ce ta farko da ta bayyana manyan tsare-tsaren kasar a fannin tsaron kasa.
Takardar bayanin mai kunshe da kalmomi kimanin dubu 9, an gabatar da ita da harsunan Sinanci da Ingilishi, da Faransanci, da yaren Rasha. Sauran yarukan su ne Jamusanci, da yaren kasar Sifaniya da Larabci, da kuma yaren kasar Japan.
Kaza lika takardar na kunshe da sassa 6, ciki hadda gabatarwa, da yanayin tsaro da ayyukan soja, da dawainiyar aikin soja, da manufofin kare kai, da na raya aikin soja, da ayyukan share fagen aikin soja, da kuma hadin gwiwar da ake yi game da aikin soja. (Lami)