in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan Amurka za ta dauki matsayin lumana kan bunkasuwar aikin sojan kasar
2015-05-11 10:03:07 cri

A jiya Lahadi, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hua Chunying ta yi bayani ga manema labarai ra'ayin kasar Sin game da rahoton da kasar Amurka ta gabatar kan batutuwan bunkasuwar aikin soja da tsaro da suka shafe ta na shekarar 2015.

A cikin bayanin Madam Hua ta ce, kasarta tana fatan kasar Amurka za ta kawar da ra'ayin yin yakin cacar baki da daukan matsayi cikin lumana da adalci kan bunkasuwar aikin soja ta kasar Sin, da kuma dakatar da gabatar da irin wannan rahoto.

Ma'aikatar tsaro ta kasar Amurka ta bayar da rahoton bunkasuwar aikin soja da tsaro game da kasar Sin na shekarar 2015 a kwanan baya, inda aka nanata barazanar da kasar Sin za ta haifar a fannin aikin soja, kuma an mai da hankali sosai kan bunkasuwar aikin soja ta kasar, da cewa matakan da kasar Sin ta dauka a tekun kudancinta sun hallaka halin da ake ciki a yankin.

Madam Hua ta kara da cewa, kasar Sin ta nace ga hanyar shimfida zaman lafiya da neman samun bunkasuwa cikin lumana, kuma ta yi ta daukar matakin kare kai, sannan ita kasa ce mai karfi wajen kiyaye zaman lafiya a yankin Asiya da Pacific da kuma duk duniya. A don haka kasar Sin tana raya aikin soja da tsaro ne domin tabbatar da mulkin kai da cikakken mulki da yankin kasar, wannan shi ne ikon da wata kasa ta dauka yadda ya kamata.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China