Game da wannan rahoto, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkoin wajen kasar Sin ta bayyana a wani taron manema labaru da aka shirya yau Alhamis cewar, yawan kudin da kasar Sin ta kashe a bangaren aikin soja a shekarar 2014 bai kai kashi 1.5 cikin kashi dari ba bisa jimillar GDP ta kasar, ba ma kawai ya yi kasa da na sauran muhimman kasashen duniya ba, har ma bai kai matsakaicin matsayi na kashi 2.6 cikin kashi dari na duk duniya ba.
Game da batutuwan kudin da kasar ke kashewa a bangaren aikin soja da karfin rundunar sojan kasar Sin da suke jawo hankulan sauran kasashen duniya, madam Hua Chunying ta jaddada cewa, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan matsayin neman ci gaba cikin lumana da manufar tsaron kasarta. Makasudin bunkasa aikin sojan kasar Sin shi ne tabbatar da dinkuwar kasar Sin gaba daya da cikakken yankunan kasar da kuma biyan bukatun neman ci gaba a yayin da take kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wasu yankunan shiyya-shiyya, har ma a duniya baki daya. Kasar Sin ta bunkasa aikin sojanta ne ba domin kawo barazana ga kowace kasa ba. (Sanusi Chen)