in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Amurka za su gudanar da tattaunawar tsaro na shekara-shekara karo na 15
2014-09-25 20:21:09 cri
Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin Geng Yanshang ya bayyana cewa, kasar Sin da Amurka za su gudanar da taron shekara-shekara kan harkokin tsaro karo na 15.

Mr Geng wanda ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai na wata-wata a nan birnin Beijing, ya ce za a gudanar da tattaunawar ce a tsakiyar watan Oktoban wannan sheakara a birnin Washington na kasar Amurka, inda mataimakin babban hafsan sojojin kasar Sin Wang Guanzhong zai jagoranci tattaunawar da mataimakiyar sakataren tsaron Amurka Christine E. Wormuth.

A yayin wannan tattaunawa ce kuma ake saran sassan tsare-tsaren ma'aikatun biyu za su yi ganawarsu ta farko.

A ranar 9 ga watan Satumban shekarar 2013 ne aka yi tattaunawar da ta gabata. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China