Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan yau yayin ganawa da jami'an sojojin kasar, ya ce, JKS na dora muhimmanci kana abin da ya kira "harkokin diflomasiya kan aikin soja", matakin da a cewarsa, ya taka gagarumar rawa wajen bunkasa ayyukan diflomasiyar kasar Sin tare da inganta matakan tsaron kasar.
Don haka ya ce, kamata ya yi hukumomin sojan kasar su kasance masu martaba shugabannin jam'iyya sau da kafa yayin gudanar da ayyukan diflomasiya na soja, karfafa musaye-musayen harkokin soja tsakanin kasa da kasa kamar yadda manufofin tsaro da diflomasiyar kasar Sin suka tanada.
Daga karshe shugaba Xi ya bukaci sojojin, da su kasance masu da'a sannan su guji karbar cin hanci da rashawa. (Ibrahim Yaya)