in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ba za ta lamunci a keta mata 'yancin yankunanta ba
2015-05-27 20:37:46 cri

Kwanan baya, dangane da tanade-tanaden da ke cikin takardar bayani da kasar Sin ta gabatar kan aikin sojinta, wato kara mai da hankali kan gwagwarmayar da ake yi a teku, sakataren gwamnatin kasar Yoshihide Suga ya ce, za a yi kokarin kaucewa amfani da karfin soja.

Dangane da lamarin, Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a nan Beijing yau Talata cewa, Sinawa sun fi darajanta zaman lafiya, saboda ba sa kaunar abin da zai kai ga shiga yake-yake. Kasar Sin na nacewa kan bin manufar raya kasa cikin ruwan sanyi da kuma manufar kare kanta daga duk wani harin da za a iya kawo mata daga waje. Amma tarihi ya ilmantar da jama'ar Sin cewa, tilas ne kasar Sin ta kara karfin kare kanta, wanda ke dacewa da raya kasa da kuma kiyaye tsaron kasa.

Don haka kasar Sin ba za ta yarda wata kasa ta zalunce ta ko keta mata 'yancin yankunanta ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China