in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi liyafar bikin ranar kafa rundunar soja a ofishin jakadancin Sin dake Senegal
2015-07-30 10:54:47 cri
Ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Senegal ya yi liyafar bikin ranar kafa rundunar sojan kasar Sin a birnin Dakar jiya Laraba 29 ga wata. A yayin liyafar, an taya babbar murnar cikon shekaru 88 da kafuwar rundunar sojan kwatar 'yanci na jama'ar kasa ta Sin, inda hafsan musamman na shugaban kasar Senegal Cheikh Gueye da wasu walikan rundunar sojan kasar Senegal da kuma manyan jami'an ofisoshin jakadanci masu kula da harkokin soja na kasa da kasa dake kasar Senegal kimanin mutane guda 50 sun halarci wannan liyafa.

Mataimakin babban jami'in kula da harkokin soji na ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Senegal, laftana kanar An Yanjun ya ba da jawabi a wajen bikin, inda ya ce, hadin gwiwar aikin soja shi ne wani muhimmin aiki cikin harkokin hadin gwiwar kasar Sin da kasar Senegal, a 'yan shekarun nan, an sami babban ci gaba kan hadin gwiwar aikin soja dake tsakanin kasashen biyu, ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Senegal ya kafa ofishin wakilin rundunar soji a hukunce a watan Yuni na bana, lamarin da zai iya inganta dangantakar sojojin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.

Kana, a matsayinta da aka taba yi mata laifi a yayin yakin Fascist, kasar Sin na son zaman lafiyar duniya, shi ya sa, sojojin kasar Sin na shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD da kuma ayyukan samar da taimakon jin kai cikin himma da kwazo, haka kuma, kasar Sin ta nuna aniyarta sosai wajen halartar babban aikin hadin gwiwar tsaron kasa da kasa da na shiyya-shiyya, da kuma kiyaye zaman lafiyar kasa da kasa da kuma na shiyya-shiyya.

A nasa bangaren kuma, Cheikh Gueye ya ce, kafuwar ofishin wakilcin rundunar soji a ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Senegal za ta iya karfafa musanyar kasashen biyu kan harkokin soji, ziyarar juna tsakanin shuwagabannin kasashen biyu, da kuma habaka hadin gwiwarsu kan ba da horaswa ga ma'aikatan da abin ya shafa. A 'yan shekarun nan, dangantakar abokantaka da hadin gwiwar dake tsakanin sojojin kasashen Sin da Senegal na zurfafa cikin yanayi mai kyau, ana inganta musanyar ra'ayoyinsu a fannonin da abin ya shafa yadda ya kamata, lamarin da zai amfanawa kiyaye zaman lafiyar kasa da kasa sosai. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China