in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jihar Xinjiang ta kasar Sin ta kara samar da naman rago domin musulmai su gudanar da sallar idi
2015-07-14 19:07:34 cri

Gwamnatin jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur na samar da naman rago da ta a tanada musamman domin karamar sallah da za a fara ba da jimawa ba ga musulmi masu Azumi a birane da garuruwa 39 na jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin jihar za ta kafa wasu shaguna kusan 200 wadanda za su samar da naman rago da yawansa ya kai kimanin ton 1000 tsakanin ranekun 13 zuwa 17 ga watan Yuli.

Ofishin kula da harkokin kasuwanci na jihar ya bayyana cewa naman da ake samarwa a wannan karo ya kai kudin Sin RMB 40 zuwa 44 kowane kilogram, adadin da ya yi kasa da na kasuwa da RMB 10 zuwa 15 bisa kowane kilogaram.

Ban da wannan kuma, an ce gwamnatocin wasu yankuna da birane, da gundumomi a jihar, za su bada tallafin kudi domin samar da nama, da ganyaye tare da 'ya'yan itattuwa, da dai sauran kayayyakin amfanin yau da kullum.

Ana dai tanadar irin wadannan tsare-tsare ne na samar da sassauci ga al'umma ne domin dakile hauhawar farashin kayayyaki. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China