Bayan abkuwar girgizar kasa, jihar Xinjiang ta fitar da shirin ko ta kwana a matsayi na biyu, wadda ta tura rukunin ma'aikata zuwa wurin da ake fama da bala'in, tare da kebe kudin agaji yuan miliyan 20 ga wannan yanki. Ya zuwa yanzu, an isar da tantuna sama da 1500, da barguna 2000, da tufafin masu tare sanyi 2000 da sauransu a yankin dake fama da bala'in. Har ila yau , an tura wata tawagar likitoci da ke kunshe da motocin ba da jiyya 9 da likitoci kwararru 33 daga birnin Urumqi, hedkwatar jihar, zuwa wurin, yayin da hukumar kula da bala'in girgizar kasa ta yankin Xinjiang ta tura rukunoni biyu da ke kunshe da ma'aikata 20 zuwa wurin cikin gaggawa domin gudanar da ayyukan tinkarar bala'in.(Fatima)