in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin "Ziri daya da hanya daya" na sa kaimi ga Xinjiang da ta gaggauta raya kasuwannin cinikin amfanin gona a Turai da Asiya
2015-04-12 16:52:23 cri

Sakamakon kaddamar da shirin "Ziri daya da hanya daya" ya sa jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin ta nuna fifiko sosai a fannonin aikin gona da fasahar shuke-shuke, a matsayinta na cibiyar hanyar siliki, kuma in an kwatanta ta da kasashen dake makwabta Uygur. Don haka tana fuskantar makoma mai kyau wajen yin hadin gwiwa da su ta fuskar aikin noma. Sabili da haka jihar Xinjiang ta gaggauta raya kasuwannin da ke nahiyoyin Turai da Asiya, lamarin da ya samar mata sabon zarafi wajen yin hadin gwiwa da kasashen ketare ta fuskar aikin gona.

A yayin taron tattaunawa karo na 2 na kasashen Asiya da Turai kan fasahohi da injuna na aikin gona kuma taron karo na farko na sayen amfanin gona a tsakanin kasa da kasa, wanda aka gudanar da shi a kwanan baya, mabambantan fasahohi da injuna na aikin gona da amfanin gona irin na kasar Sin sun jawo hankalin kamfanoni fiye da 160 na kasashen Tsakiyar Asiya da Rasha. A cikin kwanaki 2 kawai kamfanoni 20 na gida da na wajen kasar Sin sun sa hannu kan kwangilolin da darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan dari 2, yayin da darajar kwangilolin da kamfanonin Sin suka daddale ta kai kudin Sin yuan biliyan 6 da miliyan dari 2 da 50.

A shekarun baya, jihar Xinjiang tana hada kai da kasashen Tsakiyar Asiya da kasashe makwabta a fannonin kiwon dabbobi, yin amfani da ruwa da ban ruwa, yin rigakafi da kuma kashe kwari da dai sauransu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China