in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yankin Xinjiang ya bayar da lada ga wadanda suka gano 'yan ta'adda
2014-08-04 15:11:52 cri
Hukumomi a yankin Xinjiang na Uygur mai cin gishin kansa dake yammacin kasar Sin sun bayyana cewa za'a bada kyauta har fiye da Yuan dubu dari 3, kusan dalar Amurka miliyan 48 ga wadanda suka taimaka aka gano wasu mutane da ake zargi da aikata ta'addanci.

A ranar 27 ga watan Yuli ne 'yan sandan yankin suka gano 'yan ta'addan bayan da jama'a farar hula suka bada gudumuwarsu wajen gano wadanda ake zargi da ta'addanci, kuma ranar Jumma'a, sai jama'ar suka gano wadanda ake zargi a wata gonar masara dake garin Purgakqi a yankin Karakax.

Tare da taimakon jama'ar masu aikin saka fiye da dubu 30, sai 'yan sandan suka bi wadanda ake zargi da gudu har zuwa wani gida da ba kowa a cikinsa inda wadanda ake zargi suka ki amincewa a kama su, kuma sai kawai suka jefa wa jama'a bam daga nan sai 'yan sanda suka maida masu wuta kuma nan take aka kashe 9 daga cikin wadanda ake zargi da aikata ta'addanci kuma an kama mutum guda daga cikinsu.

Jami'an gwamnati fiye da dubu 10, da jama'ar gari sun halarci wani buki na bada ladan karo na farko, ga jama'ar da suka taimaka aka gano wadanda ake zargi da ta'addancin a ranar Lahadi

Gaba daya an bada yuan miliyan 4.23 a wajen bukin ga jama'ar da suka nuna jaruntakarsu wajen gano wadanda ake zargi da aikata ta'addanci.

Mutane shida wadanda suka bayar da muhimman bayanai da ya yi sanadiyyar gane maboyar 'yan ta'addan sun sami ladar yuan dubu 100 ko wannensu.

Haka zalika jama'a da dama da hukumomin jami'an gwamnati su ma an ba su kyuatuka dabam-dabam. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China