Ana kiran yankin dake kudu da tsaunukan Tianshan a jihar Xinjiang da sunan yankin Xinjiang ta kudu, wanda ya hada da Kashgar, Hotan, Kizilsu Kirghiz da kuma Aksu. Kana shi ne yanki da 'yan kabilun Uygur, Kirgiz, Mongolia, da Tajik da sauran kananan kabilu ke zaune. A sakamakon rashin bunkasuwar tattalin arziki da sadarwa, shi ya sa yankin ke fuskantar koma bayan ilmi.
An ce, tun daga shekarar bana, gwamnatin tsakiya ta kasar ta baiwa ko wane dalibi dake makarantar sakandare kudin karatu na Yuan 600 a kowane zangon karatu, kana dalibai daga kauyuka ko wadanda ke fuskantar mawuyacin halin rayuwa a birane wadanda ba su iya sayen littattafan karatu na shekaru 3 wato Yuan 1300, kuma hukumar kudi ta yankin ko karamar hukumar kudi za su baiwa kowanen dalibi kudin dakin kwana a makaranta da Yuan 600 a kowace shekara. (Zainab)