Bayanin da aka gabatar ya shaida cewa, harin na Shache na ranar 28 ga watan da ya gabata, hari ne na ta'addanci, wanda kungiyoyin ta'addancin dake kasashen waje suka taimaka wajen kitsa shi, bayan shiri na tsahon lokaci.
Kaza lika bayanin ya ce harin ya haddasa rasuwar mutane 37, wadanda ba su san hawa ba ba su san sauka ba, baya ga wasu karin mutane 13 da suka ji raunuka. Har ila yau 'yan ta'addan sun lalata motoci 31, ciki hadda guda 6 da suka kone su kurmus.
Abkuwar harin ke da wuya ne dai sai 'yan sanda suka mayar da martani ba tare da bata lokaci ba, inda suka harbe 'yan ta'adda 59, suka kuma kame wadanda ke da hannu cikin shiryawa su 215. An kuma kwace wasu wukake da gatura masu yawa, wadanda 'yan ta'addan suka yi amfani da su wajen saran mutane.
Haka kuma, jami'ai masu bincike kan lamarin, sun gano cewa, wani mutum mai suna Nuramat Sawut ne jagoran wannan mummunan aikin, wanda ya hada baki da kungiyar 'yan ta'adda ta ETIM, don yayata ra'ayin ta'addanci, da ballewar kasa tsakanin mutane, tare kuma da tsara shirin kai harin. (Bello Wang)