Hanyar jirgin kasa, mai tsawon kilomita 530, da aka gina domin saurin gudu na fiye da kilomita 200 a duk awa guda na daya daga cikin hanyoyin jiragen kasa masu saurin gudu ta Lanxin bisa tsawon kilomita 1776 dake hada Urumqi zuwa Lanzhou, hedkwatar lardin Gansu dake arewa maso yammaci, da za ta fara aiki a karshen shekarar 2014.
Wannan hanya ta jirgin kasa, dake ratsa babbar hamadar Gobi da kuma yankunan dake fama da iska, za ta hade da layin jiragen kasa masu saurin gudu dake samun habaka a kasar Sin, domin daukar muhimmin matsayi wajen kafa yankin tattalin arziki na hanyar siliki, wani babban aikin da kasar Sin take kaddamar domin bunkasa dangantaka tare kasashen Asiya na tsakiya da yammaci. (Maman Ada)