A daren ranar 30 ga watan Afrilu na bana ne, wasu mutane suka tayar da wani bam a shigar tashar jiragen kasa ta birnin Urumqi, wadda ta haddasa mutuwar mutane uku, ciki har da wani fararen hula guda daya da kuma maharan guda biyu, kana mutane 79 sun ji rauni, guda 4 a cikinsu sun ji rauni mai tsanani.
Sa'an nan a safiyar ranar 22 ga watan Mayu, wani bam ya tashi a wata kasuwa dake titin Gongyuan dake birnin Urumqi, lamarin da ya haddasa mutuwar fararen hula 39, kana wasu mutane 94 suka ji rauni.
A ranar 23 ga watan Mayu, an samu nasarar kama mutane biyar din da ake zargi da aikata laifin sai dai hudu daga cikinsu sun mutu yayin da suke kokarin tayar da bam din, koda ya ke a daren ranar 22 ga watan Mayu an kama sauran cikon na biyar din da ke tsara yadda za su wadannan hare-hare. (Zainab)