in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta fitar da farar takarda game da nasarorin da kamfanin XPCC ya cimma
2014-10-05 16:34:41 cri

A yau Lahadi ne gwamnatin kasar Sin ta fitar da wata farar takardar da ke bayani dalla-dalla game da tarihi da nasarorin da ma'aikatan noma da raya yankin Xinjiang (XPCC) suka cimma, yayin da suke bikin cika shekaru 60 da kafuwarsu, inda aka bayyana irin rawar da suka taka wajen samar da zaman lafiya a cikin al'umma da tabbatar da tsaron kan iyaka.

A cewar takardar wadda ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya wallafa, har kullum manufar gwamnatin tsakiya ita ce taimakawa ci gaban wadannan ma'aikata.

Bugu da kari takardar ta bayyana cewa, a halin yanzu yankin Xinjiang yana cikin wani muhimmmin yanayi na samun zaman lafiyar al'umma da da siyasa, kuma karkashin sabon yanayin da ake ciki, kamata ya yi a kara wa ma'aikatan yankin na Xinjiang karfi.

Takardar ta kuma yi karin haske game da yadda aka kafa, bunkasa, nauyi da zayyana tsarin rukunin ma'aikatan, sannan da rawar da yake takawa wajen bunkasa tattalin arzki, kare yankunan kan iyaka, tabbatar da zaman lafiya da bunkasa hadin kan kabilu da ke yammacin kasar.

Tun lokacin da aka kafa rukunin shekaru 60 da suka gabata, ya zuwa yanzu rukunin ya yi nasarar zamanantar da yankin na Xinjiang ta fuskantar aikin gona da masana'antu, tare da kafa sabbin birane da garuruwa ta hanyar hada kai da dukkan kungiyoyin kabilu da ke yankin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China