in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da firaministan Kamaru
2015-06-19 20:48:25 cri

A yau Jumma'a 19 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Kamaru Philemon Yang a babban dakin taron jama'ar kasa dake birnin Beijing.

A yayin ganawarsu, shugaba Xi Jinping ya ce, kasar Kamaru abokiyar arziki ce ta kasar Sin, don haka Sin take mai da hankali sosai kan bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma ta gamsu sosai kan ci gaban da aka samu ya zuwa yanzu

Har ila yau, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, a halin yanzu, kasar Sin da kasashen Afirka suna daukar nauyi na iri daya wajen neman bunkasuwa, shi ya sa, kasar Sin ke son karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen Afirka, domin cimma moriyar juna bisa fannoni daban daban. Haka kuma, ya ce kasar Sin za ta goyi bayan kasashen Afirka wajen kyautata kwarewarsu kan neman ci gaba, da kuma ciyar da dangantakar abokantaka dake tsakaninta da nahiyar ta Afirka bisa manyan fannoni gaba, ta yadda za a iya ba da karin tallafi ga jama'ar bangarorin biyu.

A nasa bangaren firaministan na kasar Kamaru, Philemon Yang ya ce, kasarsa na mai da hankali sosai kan dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, kuma a tsaye take tsayin daka kan goyon bayan manufar Sin daya tak a duniya. Daga nan sai ya bayyana godiyar kasar ta Kamaru sosai kan goyon baya da taimakon da kasar Sin take ba ta wajen raya tattalin arziki da zaman takewar al'ummarta. Ya tabbatar da cewa, kasar Kamaru tana son ci gaba da inganta dangantakar kasashen biyu, da kuma habaka hadin gwiwarsu bisa fannonin masana'antu, kayayyakin more rayuwa, ba da ilmi da dai sauransu.

Kaza lika, ya ce, kasar Kamaru na son ba da gudummawa wajen ciyar da hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka gaba, bisa tsarin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka.

Haka shi ma a wannan rana, shugaban majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin Yu Zhengsheng ya gana da firaminista na kasar Kamaru Philemon Yang a nan birnin Beijing. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China