in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya gana da takwaransa na Kamaru
2015-06-18 21:37:06 cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da takwaransa na kasar Kamaru Philemon Yang, wanda ke ziyarar aiki a nan kasar Sin.

A yayin ganawar ta su da yammacin yau Alhamis din nan, Li Keqiang ya ce kasar Sin na dora muhimmancin gaske, game da bunkasa huldar ta da kasar Kamaru, ta na kuma fatan kara bunkasa amincewa da juna tsakanin ta da Kamaru, tare da kuma karfafa hadin gwiwa a sauran fannoni.

Mr. Li ya kara da cewa ya na fatan kasashen biyu za su kara tuntubar juna a harkokin duniya da na shiyya shiyya, tare da dada bunkasa huldar kasashen biyu.

Mr. Li Keqiang ya jaddada cewa, karfafa hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afirka, da ma sauran kasashe masu tasowa baki daya babban tushe ne cikin manufofin diplomasiyyar kasar Sin.

A nasa bangare, Mr. Yang cewa yayi huldar da ke tsakanin Kamaru da Sin ta zama kyakkyawan misali na irin huldar da ta dace tsakanin kasashen duniya, duba da yadda kasashen biyu suka cimma dimbin nasarori a fannonin hadin gwiwarsu. Ya kara da cewa, Kamaru na fatan ci gaba da kokari wajen ciyar da huldar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka gaba.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China