A lokacin wani taron manema labarai da ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta kira a yau Litinin 4 ga wata, a dangane da bikin da shugaba Xi zai halarta, Mr Cheng Guoping ya yi bayani cewa, wannan shekara ta cika shekaru 70 da al'ummar Sinawa suka cimma nasarar yakin kin harin Japan kana ta cika shekaru 70 da samun nasara a kan 'yan fascist a duniya baki daya.
Yace kasashen Sin da Rasha muhimman fagen yaki ne a Asiya da Turai, kuma su ne wakilan kasashen da suka cimma nasara a yaki da kuma mambobin farko da suka kafa MDD, sannan sune zaunannun mambobin kwamitin sulhu na majalisar, sun kuma ba da taimako matuka a yakin duniya na biyu.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci wannan gaggarumin biki da ragowar ayyuka, ciki hadda duba faretin sojojin Rasha, da wasu bukukuwa da sauransu.
Cheng Guoping ya kuma yi bayanin cewa, ziyarar shugaba Xi a wannan karo na da zummar kiyaye zaman lafiya, samun makoma mai kyau cikin hadin gwiwa, sannan kuma da zurfafa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da ta Rasha.
Har wa yau, wannan ziyara zuwa ga kasar Kazakhstan shi ne karo na biyu bayan shekara daya da shugaban ya yi, wanda ya bayyana cudanya mai kyau tsakanin kasashen biyu, tare da alamanta cewa, Sin da Kazakhstan na kara daga dangantakar dake tsakaninsu zuwa sabon matsayi da kara amincewa da juna.
Ban da haka kuma, game da ziyarar shugaba Xi a kasar Belarus, Mr.Cheng yana mai cewa, wannan ya kasance karo na farko da shugaban kasar Sin ya kai ziyara a Belarus a shekaru 14 da suka gabata, kuma daidai lokacin da aka gudanar da bikin cika shekaru 70 da cimma nasarar yakin kin harin Japan da yakin kin ra'ayin nuna karfin soja, abin da ya kawo ma'ana sosai ga hada yanayin da da na nan gaba ta fuskar dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu da bude sabbin shafuna a wannan fanni. (Amina)