Bisa ajandar da aka tsara, a wannan rana da misali karfe 9 da minti 20, shugabannin kasashen Asiya da Afrika sun taka sayyada daga otel din Savoy Homann zuwa ginin Gedung Merdeka wato inda aka shirya taron Bandung a lokacin baya, wannan tafiya tana da ma'anar tarihi, saboda kafin shekaru 60 da suka wuce, tsoffin shugabannin kasashen Asiya da Afrika sun yi wannan tafiya ne, don halartar taron. A ranar yau, shugabannin kasashen Asiya da Afrika, sun yi tafiyar ne domin tuna da tarihi, da kuma yada akidar hadin gwiwa, sada zumunta da sauransu.
Daga bisani kuma, an yi bikin tunawa da taron Bandung a cikin ginin Gedung Merdeka.(Bako)