Kana bisa gayyatar da shugaban kasar Rasha Vlładimir Putin ya yi masa, shugaba Xi Jinping zai kai ziyara a kasar Rasha tare da halartar bikin cika shekaru 70 da kawo karshen yakin Soviet da Jamus daga ranar 8 zuwa 10 ga wata a birnin Moscow.
Sannan kuma, bisa gayyatar da shugaban kasar Belarus Alexandr Lukashenko ya yi masa, shugaba Xi Jinping zai kai ziyara kasar ta Belarus tun daga ranar 10 zuwa 12 ga wannan wata. (Zainab)