in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya gabatar da shawarwari 3 game da ciyar da manufar Bandung gaba
2015-04-22 15:49:55 cri

Shugaba Xi Jinping na nan kasar Sin, ya gabatar da wasu muhimman shawarwari 3, game da burin ciyar da manufar Bandung gaba.

Shugaban wanda ya gabatar da wadannan shawarwari yayin da yake tsokaci gaban mahalarta taron koli na Asiya da Afrika dake gudana a kasar Indonesiya, ya kuma yi kira ga daukacin kasashen nahiyar Asia da Afirka, da su rungumi manufofin Bandung, tare da aiki tare a fannin gina al'ummar duniya mai cike da nasara ga kowa.

Shawarwarin wadanda shugaba Xi ya gabatar na da burin cimma nasarar hadin kai, da abuta mai inganci tsakanin kasashen duniya, matakan da ke da matukar muhimmanci ga duniyar yau, wadanda kuma suka dace da manufar ta Bandung. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China