Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan yayin wani zaman nazari da mambobin zaunannen kwamitin hukumar siyasa na JKS suka gudanar a ranar Alhamis, ya kara da cewa burin mahukuntan kasar ne su ga manoma dake karkara, sun samu damar ba da tasu gudummawa a harkokin ci gaban kasa, sa'an nan su samu cikakkiyar damar cin gajiya, daga nasarorin da kasar ke samu.
Kaza lika shugaba Xi ya ce batun gina sabuwar kasar Sin mai cike da nasarori, ya ta'allaka ga yadda aka daidaita ci gaban birane da karkara ta fuskar tattalin arziki, da batun samar da damammakin kasuwanci, da na rabon albarkatu tsakanin sassan biyu.
Ya ce duk da muhimmnacin burin kasar Sin na samar da matsakaicin ci gaba, a dukkanin fannonin rayuwar al'umma nan da shekarar 2020, a hannun guda wannan kuduri na fuskantar kalubale, duba da babban gibin dake tsakanin birane da kauyuka ta fuskar yawan al'umma, musamman a tsakanin sassan kasar dake fama da talauci, da kuma biranen dake samun saurin bunkasa. (Saminu Hassan)