Yayin ganawar tasu a Alhamis din nan, shugaba Xi ya jaddada cewa, kasarsa na dora muhimmanci sosai game da alakar dake tsakaninta da Iran, kuma a cewarsa, kwanan baya, Iran da kasashe 6 sun cimma matsaya guda game da batun nukiliyar Iran a zaman shawarwarin da suka gabata, wanda hakan ya sa ana samu ci gaba wajen daddale yarjejeniya daga dukkanin fannoni a tsakanin bangarori daban daban.
Shugaba Xi ya ce, kasarsa na fatan ci gaba da tuntubar bangarorin da abun ya shafa, ciki har da kasar Iran, don ci gaba da ba da gudummawa game da shawarwarin nukiliya, a wani mataki na daddale yarjejeniya cikin adalci da cimma moriyar juna.
A nasa bangare shugaba Rouhani, ya ce, yana farin cikin sake samun damar ganawa da shugaban Xi, domin yin musayar ra'ayoyi game da muhimman batutuwan da suke mai da hankali a kai. (Bako)