in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping ya gabatar da jawabi ga mahalarta bikin baje-koli na Milano
2015-05-02 16:21:50 cri
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya bayyana irin muhimmancin da kasarsa ke baiwa harkar noma, ta hanyar amfani da sabbin dabarun kimiyya da fasahohin zamani, matakin da ya baiwa kasar damar ciyar da al'ummarta sama da su biliyan 1 da miliyan dari 3.

Shugaban na Sin wanda ya bayyana hakan yayin bude rumfar nune-nune ta kasar Sin, a harabar filin da aka ware domin bikin baje-kolin harkokin noma na bana da aka yiwa lakabi da Expo-Milano, wanda kuma ke gudana a birnin Milan na kasar Italiya.

Xi wanda ya gabatar da jawabin ta kafar sadarwar internet, baya ga maraba da ya yi wa mahalarta rumfar ta Sin, ya kuma kara da cewa bikin baje kolin na Milano na mai da hankali ga harkokin da suka jibanci noma da samar da abinci, da ma dabarun inganta rayuwar jama'a a wannan fanni. Don haka a cewarsa bikin na da matukar alfanu ga rayuwar bil' Adama.

Ya ce ga dukkanin wadanda suka halarci rumfar kasar Sin, za su dada fahimtar matakan da kasar ta dauka a fannin raya harkokin noma, da inganta sarrafa abinci, fannonin da a cewarsa na da matukar tasiri ga ci gaban da kasar ta samu a dukkanin fannoni.

Kaza lika shugaban na Sin ya bayyana irin kwazon da gwamnatinsa ke yi, wajen raya harkar noma a yankunan karkara, yana mai cewa a wannan gaba da Sin ke samun babban ci gaba wajen zamanintar da ayyukan noma, tana da burin yin musayar dabaru, da kwarewa da sauran sassan duniya, matakin da zai tabbatar da wadatar abinci, da inganta rayuwar bil'adama baki daya. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China