in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da taron koli na Asiya da Afrika a Indonesiya
2015-04-22 11:30:33 cri

A safiyar yau Laraba ne, aka kaddamar da taron koli na Asiya da Afirka a cibiyar taro dake birnin Jakartar kasar Indonesiya, taron da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya samu halarta.

Shugabanni mahalartar taron za su tattauna game da batun gada, da kuma yada akidar taron Bandung a sabon yanayin da ake ciki, don sa kaimi ga raya hadin gwiwa, da samun bunkasuwa a kasashen Asiya da Afrika.

Gwamnatin Indonesiya ce dai, ta karbi bakuncin shirya wannan taro, kana kuma taken taron shi ne "Inganta hadin gwiwar kasashe masu tasowa da sa kaimi ga samun zaman lafiya da wadata a kasashen duniya".

Shugabanni da wakilai na gwamnatoci da kungiyoyi kimanin 100 ne suke halartar wannan taron. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China