A cewar minsitan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, wannan ziyarar aiki da shugaban na Sin ya gudanar tsakanin ranekun 20 zuwa 24 ga wata, ta alamta burin da Sin ke da shi na tabbatar da hadin kai tsakanin kasashen duniya, da kuma kudurin samun makoma ta bai daya tsakanin ta da makwaftanta, da ma burin cimma nasarar aiwatar da sabon salon dangantakar kasa da kasa.
Ya ce ziyarar ta kuma nuna fatan da ake da shi na karfafa hulda tsakanin kasar Sin da kasashen biyu, da kuma huldar ta da sauran sassan duniya baki daya, musamman ma game da batutuwan da suka jibanci siyasa da tattakalin arziki.
Mr. Wang ya kara da cewa kasar Sin ta bada babbar gudummawa ga nasarar taron Bandung da aka gudanar a karon farko a shekarar 1955, taron da ya maida hankali ga batun karfafa hadin gwiwa tsakanin kasahen Asiya da na Afirka, da kuma sauran kasashen masu tasowa.
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya ce babban al'amari ne, ganin yadda bayan shekaru 60, shugabannin Asiya da na Afirka suka sake haduwa a Indonesia, domin gudanar da wannan taro mai matukar muhimmanci, wanda a wannan karo ya maida hankali ga zakulo hanyoyin bunkasa tunanin taron na Bandung, wato batun hadin kai, da abuta, da kuma marawa juna baya.(Saminu)