A yayin ganawar, shugaba Xi Jinping ya yi maraba da zuwan tawagar jam'iyyar KMT, inda ya bayyana cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da jam'iyyar KMT da jama'ar gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan sun yi kokari tare wajen kawo haske ga makomar samun zaman lafiya da bunkasuwa a tsakanin gabobin biyu, da kawo moriya ga juna, lamarin da jama'ar gabobin biyu suka nuna goyon baya da amincewa da shi, kana kasashen duniya suka yaba da shi.
Shugaba Xi ya jaddada cewa, an fuskanci wahala wajen samu ci gaban shimfida zaman lafiya da samun bunkasuwa a gabobin biyu. Xi ya yi nuni da cewa, a sabon halin da ake ciki, kamata ya yi jam'iyyun gabobin biyu su kara yin imani da juna da fahimtar juna, da tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa kan dangantakar dake tsakaninsu, da yin kokari tare wajen kafa kungiyarsu ta cimma buri daya. Game da wannan, Xi ya gabatar da shawarwari biyar.
Na farko, a tsaya tsayin daka kan manufar Sin daya tak da gabobin biyu suka cimma yarjejeniya a kai a shekarar 1992, da nuna adawa da yunkurin samun 'yancin kan yankin Taiwan wanda shi ne tushen siyasa na tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwar gabobin biyu, kana a amince da Sin ta mallaka babban yankin kasar Sin da kuma yankin Taiwan.
Na biyu, a zurfafa yin hadin gwiwa a tsakanin gabobin biyu don samun moriyar juna, da amfana wa jama'arsu, wannan shi ne burin raya dangantakar dake tsakanin gabobin biyu.
Na uku, yin mu'amala a tsakanin gabobin biyu shi ne yin mu'amala a tsakanin jama'arsu.
Na hudu, jam'iyyun biyu da gabobin biyu su duba halin da ake ciki a yanzu, da girmama da juna da kuma kara yin imani da juna a fannin siyasa.
Na biyar, ya kamata dukkan jama'ar kasar Sin su yi kokari tare wajen bunkasa al'ummar kasar Sin baki daya.
A nasa bangare, Zhu Lilun ya bayyana cewa, gabobin biyu su ne al'ummar kasar Sin, wadanda suke da buri iri daya. Ya zuwa yanzu an samu nasarori a kokarin da ake na samun zaman lafiya da bunkasuwa a tsakanin gabobin biyu, yana fatan gabobin biyu za su ci gaba da yin hadin gwiwa a fannonin tabbatar da zaman lafiya da kiyaye muhalli da tattalin arziki da dai sauransu bisa tushen manufar da aka cimma daidaito a kai a shekarar 1992, jama'a da kanana da matsakaitan kamfanoni da kungiyoyin matasa na gabobin biyu za su amfana, da kuma ci gaba da sa kaimi ga samun zaman lafiya da bunkasuwa a tsakaninsu. (Zainab)