in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin zai halarci bikin bude taron kungiyar shawarwari kan harkokin shari'a na Asiya da Afrika karo na 54
2015-04-07 20:26:03 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang zai halarci bikin bude taron shekara shekara na kungiyar shawarwari kan harkokin shari'a na Asiya da Afrika karo na 54, taron da zai gudana daga ran 13 zuwa 17 ga watan Afrilu, a nan birnin Beijing.

Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Hua Chunying ta sanar da hakan a taron manema labaru da aka yi a yau Talata 7 ga wata a nan birnin Beijing, inda ta nuna cewa, kasashen kungiyar da dai sauran kunyiyoin kasa da kasa dake da nasaba da wannan batu za su tura tawagoginsu don halartar taron.

Haka kuma, madam Hua ta ce, yayin taron, za a kuma kira taron musamman na tunawa da cika shekaru 60 da taron Bandung da kuma taron kara juna sani kan tsarin dokokin MDD da zaman oda bayan babban yakin duniya na biyu.

An ba da labari cewa, kungiyar ta kafu ne a shekarar 1956 bisa tunanin da aka samar cikin taron Bandung da aka yi a shekarar 1955, da zummar sa kaimi ga kasashen Asiya da Afrika da su kara musayar ra'ayoyi da juna kan batun dokokin duniya ta yadda za a bayyana bukatunsu cikin a yayin bunkasuwar dokokin. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China