Kwanan baya, majalisar gudanarwa ta kasar Amurka ta nuna cewa, ya kamata kasar Sin ta saurari ra'ayin kasarta a yayin da Sin ta kafa daftarin dokar yaki da ta'addanci. Dangane da lamarin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a yau cewa, kafa dokar yaki da ta'addanci harkar cikin gidan kasar Sin ce, babu bukatar ta saurari ra'ayoyin kasashen ketare, haka kuma, kasashen ketare ba su da ikon matsa lamba ga kasar Sin kan wannan harkar, don haka kasar Sin na fatan kasar Amurka za ta mutunta batutuwan da suka shafi yadda kasar Sin ke kafa dokokinta.
Bugu da kari Hua Chunying ta jaddada cewa, matakan da kasar Sin ta dauka domin kiyaye tsaron bayanai sun dace da ka'idar dokokin gudanar da mulki, sun kuma dace da akidar gamayyar kasa da kasa, bugu da kari, matakan ba za su kalubalanci moriyar 'yan kasuwa da ke mu'amula da intanet ba. (Maryam)